Isa ga babban shafi
CEMAC

Taron CEMAC ya cim-ma yarjejeniyar zirga-zirga ba tare da Bisa ba

Taron CEMAC na Kasashe 6 da ke tsakiya da yammacin Afirka sun cim-ma yarjejeniyar zirga-zirga tsakaninsu ba tare da amfani da takardar Bisa ba.

Taron CEMAC ya cim-ma yarjejeniyar zirga-zirga ba tare da Bisa ba
Taron CEMAC ya cim-ma yarjejeniyar zirga-zirga ba tare da Bisa ba AFP/STR
Talla

Kasashen da ke amfani da harshan Faransanci da suka hada da Kamaru da Afirka ta Tsakiya da Equatorial Guinea da Gabon da Jamhuriyar Congo sun cim-ma wannan yarjejeniyar ne a taron da su ka gudanar a birnin N’djamena na Chadi.

Sanarwar da taron ya fitar, ta ce bankin bunkasa kasashen afirka ta tsakiya zai tallafawa kasashen da CFA biliyan 1.7 domin aiwatar da shirin.

Sama da shekaru 15 da suka gabata aka soma tattaunawar cim-ma wannan yarjejeniyar, wadda a 2013 aka fitar da daftarin abubuwan da shirin zai kunsa.

Shirin a baya ya fuskanci tsaiko, daga Equatorial Guinea da Gabon da suka nuna furgaban cewa zai bude kofa ga kwararan baki masara ayukanyi kasashensu.

Sai dai daga bisani Wadanan kasashe da kuma Congo da Afirka ta tsakiya sun cim-ma matsaya kan matakan da shirin zai kunsa a watan da ya gabata. Inda Kamaru ce ta soma nuna amincewar ta.

Kasar Gabon ta ce soma aiwatar da wannan yarjejeniyar na bukatar abubuwa Uku da suka hada da amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan fasinjoji, inganta hukumomin tsaro da mutunta dokar kwadago.

Taron CEMAC ya hada kasashe ne da ke da hanyoyin samar da kudadde amma ke fuskantar koma baya wajen aiwatar da manyan tsare-tsare da sa’ido tare da bunkasa tattalin arzikinsu.

Daga cikin shirin da kasashen ke fatan aiwatarwa akwai batun samar da kamfanin jirgin sama da fasfon bai-daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.