Kotu ta danka 'ya'yan Hama Amadou a hannun gidan marayu
Kotu a birnin Yamai na Jamhuiryar Nijar ta bayar da umurnin kwace yara 16 daga cikin yara sama da 20 da aka bayyana cewa an sayo su ne daga kasashen ketare, inda kotun ta bayar da umurnin ci gaba da kula da su a wani gidan marayu da ke birnin Yamai.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Daga cikin wadanda aka kwacen har da yara biyu wadanda tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Hama Amadou ke ikirarin cewa ‘yayansa.
Yanzu haka da dama daga cikin iyayen wadannan yara na tsare a gidan yari, bayan da kotu ta same su da laifin cewa an sayo yaran ne daga Najeriya, yayin da daya daga cikin wadanda kotun ta sama da laifi a wannan batu tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Hama Amadou ya gudu daga kasar kimanin shekaru biyu da suka gabata, duk da cewa matarsa wadda ta yi ikirarin cewa ita ta haifi yara ke tsare a gidan yari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu