"Mutane miliyan 3 na fuskantar hadarin yunwa a Jamhuriyar Congo"
Shugaban hukumar bada agajin abinci ta majalisar dinkin duniya David Beasley ya bukaci manyan kasashen duniya da su kai taimako zuwa lardin Kasai na Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo da tashin hankali ya dai-daita.
Wallafawa ranar:
Beasley ya ce sama da mutane miliyan uku ne a yankin na Kasai ke fuskantar hadarin fadawa yunwa, tare da gargadin cewa muddin ba’a dauki mataki ba, dubban daruruwan yara ka iya rasa rayukansu nan da watanni kalilan.
A watan Agustan shekara ta 2016 tashin hankali ya barke a yankin na Kasai bayan mutuwar wani basaraken gargajiya, lamarin da yayi sanadin mutuwar sama da mutane 3000 da kuma raba wasu miliyan 1 da rabi da gidajensu.
Tashin hankalin yayi kamari ne bayanda wasu mayaka mabiyan mai sarautar gargajiyar Kamuina Nsapu, suka kaddamar da harin ramuwar gayya kan sojin kasar da suka zarga da kashe shugaban nasu, wanda gwamnati taki amincewa da shugabancin yankin na Kasai da yake.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu