Isa ga babban shafi
Somalia

Jami'an tsaron Somalia na zargin gwamnati da sakaci

Wani rahoton hadaka tsakanin jami’an tsaron Somalia sun zargi gwamnatin kasar da kasashen da ke mara mata baya wajen yaki da kungiyar Alshabab, da kin daukar matakan da suka dace don kare rayukan al’umman kasar.

Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a harin na makon jiya wanda aka bayyana da mafi munin hari da aka kai a Nahiyar Afrika.
Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a harin na makon jiya wanda aka bayyana da mafi munin hari da aka kai a Nahiyar Afrika. REUTERS/Feisal Omar
Talla

Rahoton dai na zuwa ne bayan harin kunar bakin waken makon jiya da ya hallaka sama da mutum 300 a birnin Mogadishu wanda kuma aka bayyana da mafi munin hari da aka kaddamar a baya bayan nan a Nahiyar Afrika.

Hussein Moalim Mohamud tsohon mashawarcin shugaban kasar kan harkokin tsaro, ya ce dukkanin kungiyoyin da ke yaki da kungiyar ta Alshabab sun gaza wajen dakile ayyukan kungiyar la’akari da yadda ta ke ci gaba da kai munanan hare-hare.

A cewar rahoton cikin shekarar da ta gabata kadai Alshabab ta kai hare hare 395 da ya lakume rayukan kusan mutum dari 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.