Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta inganta hulda da Najeriya

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, sun yi alkawarin kara inganta huldar tsaro da tattalin arziki tsakanin kasashensu bayan sun tattauna a Ankara.

Shugaban Turkiya Reccep Tayyip Erdogan tare da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari a Ankara
Shugaban Turkiya Reccep Tayyip Erdogan tare da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari a Ankara naij.com
Talla

Batutuwan da shugabannin biyu suka tattauna sun kunshi karfafa saka jari da kuma yadda Turkiya za ta taimakawa Najeriya yakar ta’addancin Boko Haram.

A lokacin da ya ke zantawa da Erdogan a fadarsa a Ankara, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kofar kasarsa a bude ta ke ga ‘yan kasuwar Turkiya masu saka jari.

A na shi bangaren Mista Erdogan ya ce Turkiya za ta yi kokarin sanya hannu kan yarjejejeniyar kasuwanci da Najeriya ta kudi fiye da dala biliyan 1.

Shugaban Najeriya ya kai ziyarar aiki ne a Turkiya inda gobe Juma’a ake sa ran  Buhari zai tafi Istanbul domin halartar wani babban taron kasashe 8 na musulmi masu tasowa da suka kunshi Masar da Indonesia da Iran da Malaysia da Pakistan da Najeriya da kuma Turkiya.

Ana sa ran shugaban da jami’an gwamnatinsa da suka masa rakiya za su yi amfani da damar domin tattauna batun makaman da hukumar Kwastam ta kama da aka ce an shigo da su ne daga Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.