Isa ga babban shafi
Kenya

Amnesty ta zargi jami'an tsaron Kenya da hallaka masu zanga zanga

Kungiyoyin kare hakkin dan’adam ta Human Rights Watch da kuma Amnesty International, sun ce ‘yan sandan kasar Kenya sun hallaka kalla mutane 33, yayin kokarin murkushe masu zanga-zanga.

Jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma a Kenya, yayinda suke tarwatsa dandazon masu zanga zanga a birnin Nairobi.
Jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma a Kenya, yayinda suke tarwatsa dandazon masu zanga zanga a birnin Nairobi. REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Zanga zangar ta barke ne tun bayan sanar da nasarar shugaba mai ci Uhuru Kenyatta, wanda daga bisani kotun kolin kasar ta soke.

Sai dai janyewar jagoran ‘yan adawa Raila Odinga daga sake sabon zaben a wannan wata, ya sake rura wutar zanga zangar.

Ga dai abinda Justus Nyang’aya Darkatan Amnesty International da ke Kenyan, ke cewa dangane da lamarin.

00:57

Amnesty ta zargi jami'an tsaron Kenya da hallaka masu zanga zanga

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.