Chadi za ta ci gaba da taimakawa a tsaron yankin Sahel
Kasar Chadi ta fara janye daruruwan dakarun ta da ke yaki da kungiyar Boko Haram a yankin Diffa, dakarun da zasu kula da tsare kan iyakokin kasar da Libya da Nijar.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Chadi ta umurci sojojinta da suka baro yankin Diffa kula da kan iyakokin kasar da Libya da Nijar a matakin shirin nan na rundunar G5.
Ministan tsaron Chadi Bichara Issa a wata zantawa da manema labarai ya bayyana cewa Chadi ba ta janye dakarun ta ba daga Nijar, matakin shine na karfafa tsaro a kan iyakokin ta da sauren kasashe, a karshe ministan ya bayyana cewa hadin guiwar rundunar kasashen za ta maye gurbin rundunar Chadi da ta fice daga yankin Diffa a Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu