Isa ga babban shafi
Kenya

Raila Odinga ya janye daga zaben Kenya

Jagoran ‘yan adawa a Kenya Raila Odinga, ya sanar da janyewa daga zaben shugabancin kasar da aka tsara gudanarwa a ranar 26 ga wannan wata na oktoba.

Raila Odinga jagoran adawa a kasar Kenya
Raila Odinga jagoran adawa a kasar Kenya REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

A sanarwar da ya yi dazun nan a birnin Nairobi, Odinga ya ce ya dauki matakin janyewar ne saboda kare muradun kasar ta Kenya da kuma na al’ummarta.

Odinga da ya nuna shakku kan yi masa adalci a zaben da za a yi a nan gaba, ya bayyana rashin gamsuwarsa da irin matakan da hukumar zabe ta kasar ke dauka.

Raila Odinga yayin sanar da janyewa daga zaben kenya da za a maimaita

A watan da ya gabata kotun kolin kasar ta soke zaben shugabanci kasa da aka gudanar a ranar 8 ga watan Agusta kuma ya bai wa shugaba mai ci Uhuru Kenyatta Nasara kan wasu kura-kurai da ta ce an tafka.

Shugaba Kenyatta ya ce bai karaya ba da wannan hukunci da Odinga ya dauka na janye takararsa.

Martanin Shugaba Uhuru Kenyatta kan janyewar Odinga daga zabe

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.