Isa ga babban shafi
Nijar

'Yan ta'adda sun kashe Sojojin Amurka a Nijar

Wasu 'yan ta’adda sun kai hari kan tawagar sojojin Amurka da Nijar da ke aiki kusa da iyakar Mali inda suka kashe sojoji da dama.

Yankin Tillabery inda aka kai hari a Nijar
Yankin Tillabery inda aka kai hari a Nijar RFI/Sayouba Traoré
Talla

Bayanan da ke fitowa dangane da harin sun ce 'Yan ta’addan sun yiwa sojojin kwantan bauna ne lokacin da suke gudanar da ayyukan su a Tilaberi.

Jaridar New York Times ta ruwaito cewar sojojin Amurka 3 aka kashe a harin tare da wasu na Nijar 5.

Wannan shine hari na farko da ya ritsa da sojojin Amurka a Nijar, wadanda suke taimakawa wajen horar da sojojin Nijar da kuma basu taimakon da ya dace kan yaki da ta’addanci.

Mai Magana da yawun fadar shugaban Amurka, Sarah Sanders ta ce an sanar da shugaba Donald Trump game da harin ba tare da Karin haske akai ba.

Wannan shine karo na farko da ake bayani kan kasasncewar sojojin Amurka a Yankin mai tattare da hadari sakamakon tashin hankalin da ake samu a Mali.

Majalisar Dinkin Duniya na da dakaru 12,500 da ke aikin samar da zaman lafiya a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.