Isa ga babban shafi
CAR

'Yan bindiga a Afirka ta Tsakiya na cin zarafin mata

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta yi zargin cewar kungiyoyin 'yan bindiga a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na cin zarafin mata da 'yam mata wajen azabtar da su da kuma musu fyade.

Mata da kananan yara na cikin wani hali a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Mata da kananan yara na cikin wani hali a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya unhcr.org
Talla

Rahotan kungiyar ya nuna cewar, ta samu korafe-korafe 305 da suka kunshi fyade da azabtarwar da aka yiwa mata da 'yam mata 296, wanda hakan kadan ne daga cikin irin tashin hankalin da ake samu.

Hillary Margolis, mai bincike kan harkokin mata a kungiyar ta ce an aikata wadannan laifufuka ne tsakanin shekarar 2013 zuwa tsakiyar wannan shekara sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan kifar da gwamnatin shugaba Francois Bozize.

Rahotan ya bayyana sunayen wasu shugabannin 'yan tawaye 6 da ke da hannu a fyaden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.