Za a yi shari’ar wasu ‘Yan Boko Haram a asirce
Rahotanni a Najeriya sun ce za a yi shari’ar wasu da ake zargi ‘Yan kungiyar Boko Haram ne a asirce ba tare da ba ‘yan jarida damar halartar zaman kotun ba.
Wallafawa ranar:
Wani Jami’ in Ma’aikatar Sharia a Najeriya ne ya shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa za a shariar ‘yan kungiyar Boko Haram 1,600.
Jami’in ya ce an tsayar da wannan shawara ne saboda matakan tsaro bayan wani tattaunawa tsakanin Jami’an Gwamnati da kuma jami’an tsaro na farin kaya.
A ranar 9 ga watan gobe ne ake sa ran fara shariar wadanda ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da ke tsare a wuraren daban-daban.
Hukuncin kare hakkin dan adam sun dade suna sukar jami’an tsaron Najeriya da kame fararen hula da sunan ‘yan Boko Haram ba tare da an gabatar da su a kotu ba
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu