Isa ga babban shafi
Ghana

Kotu ta bai wa Ghana damar hako mai a kan iyakarta ta Côte d'Ivoire

Kotun warware rikice-rikice a tsakanin kasashen duniya da ke birnin Hamburg na kasar Jamus, ta yanke hukuncin mikawa Ghana damar ci gaba da aikin hako man fetur a yankin kan iyakarta da Ivory Coast, matakin da ya kawo karshen tsawon shekarun takun-saka tsakanin kasashen biyu.

Yankin teku mai arzikin mai da Gahan ke takaddama da Cote d'Ivoire a kansa.
Yankin teku mai arzikin mai da Gahan ke takaddama da Cote d'Ivoire a kansa. ©PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Kamfanin Tullow Oil da ke gudanar da aikin bincike da hako man fetur a yankin, ya bayyana cewa zai fara aiki gadan-gadan domin hako akalla ganga dubu 80 a kowace rana daga farkon shekara mai zuwa.

Kotun karkashin jagorancin alkali Boualem ta ce Ghana bata mamaye kan iyakar Cote ‘d Ivoire ba sakamakon aikin nata na tono danyen man, kamar yadda Cote d’ Ivoiren ke ikirari a baya.

An dai shafe akalla shekaru 10 ana takaddama tsakanin kasashen biyu, kan wanda ya mallaki yankin ruwan da arzikin danyen man dana Iskar gas ke shimfide a karkashinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.