Isa ga babban shafi
Africa ta Kudu

Jacob Zuma na neman kariyar kotu kan zarge-zargen cin hanci 783

Shugaba Jacob Zuma na Africa ta Kudu ya shigar da wata bukata gaban kotun kasar yau Alhamis domin neman kariyar kotun game da zarge-zarge 783 da ake masa da suka shafi cin hanci da rashawa a shekarun baya.

shugaban kasar Africa ta kudu Jacob Zuma.
shugaban kasar Africa ta kudu Jacob Zuma. Reuters
Talla

Babbar Jam'iyyar adawa da ke kasar Democratic Alliance DA- a takaice, ta shiga kotu har sau 11 daga shekara ta 2009 domin neman an tono zargin safarar makamai a lokacin mulkin wariyar launin fata, da ake ganin Jacob Zuma na da hannu.

A shekara ta 2005 ma sai da aka tuhumi tsohon mashawarcin shugaban kan harkokin kudi Schabir Shaik da laifin karban cin hanci game da safarar makaman kuma aka zartas masa da hukuncin daurin gidan yari na shekaru 15, amma aka sallame shi daga bisani sakamakon rashin lafiya.

A lokuta da dama dai ana zargin shugaba Jacob Zuma da laifukan cin hanci da rashawa baya ga rub da ciki kan kudade da kuma halatta kudaden haram, duk da cewa dai shugaban ya sha musanta zargin tare da fadin cewa kazafi ne kawai ake yi masa.

Zuma da Gwamnatinsa ana zarginsu da karbar cin hanci da ya kai Dollar biliyan 5, wajen sayen jiragen yaki, da makamai daga kasashen turai 5 ciki har da Britania, da Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.