Isa ga babban shafi
Uganda

Uganda na son yi wa dokar tsayawa takara kwaskwarima

Jam'iyya mai mulki a Uganda na yunkurin gabatar da wata doka a zauren majalisar kasar wadda za ta soke adadin shekarun da aka kayyade wa mutun kafin cancantar tsayawa takarar shugaban kasa.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni
Shugaban Uganda Yoweri Museveni Capture d'écran al-Jazeera
Talla

Kundin tsarin mulkin Uganda ya haramta wa mutumin da ya zarce shekaru 75 tsayawa takarar shugabancin kasa, yayin da jam'iyyar shugaba Yoweri Museveni mai shekaru 73 da haihuwa ke bukatar yi wa dokar kwaskwarima.

Ana ganin cewa, jam'iyyar ta dauki wannan matakinne don bai wa shugaba Museveni damar neman wani sabon wa'adi nan gaba.

Simeo Nsubuga, dan majalisa daga Jam’iyyar National Resistence Movement ta Museveni ya ce tuni suka amince da shirin a taron jam’iyyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.