Isa ga babban shafi
Chad

Faransa ta bukaci Chadi ta gudanar da zaben 'yan majalisu

KASAR Faransa ta bukaci gwamnatin Chadi ta gudanar da zaben Yan Majalisu bayan kasashen duniya da ke bada agajin sun yi alkawarin taimaka mata da makudan kudade domin farfado da tattalin arzikinta da ke tangal tangal.

shugaban kasar Chadi Idriss Deby tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron.
shugaban kasar Chadi Idriss Deby tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron. Reuters
Talla

Kiran na Faransa ya biyo bayan ikrarin shugaba Idris Deby a watan Fabarairun wannan shekara cewar kasar bata da kudaden da zata gudanar da zaben Yan Majalisu.

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Faransa Agnes Romatet-Espagne ta shaidawa manema labarai cewar zaben Yan Majalisun na da matukar tasiri wajen tabbatar da dimokiradiya.

Ranar juma’ar da ta gabata, gwamnatin Chadi tace ta samu alkawarin tallafin da ya kai sama da Dala biliyan 18 domin bunkasa ci gaban kasar tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021, wanda ya ribanya has ashen da tayi.

Romatet-Espagne tace daga cikin kudaden Faransa zata baiwa Chadi euro miliyan 233.

Kasar Chadi ta fuskanci matsaloli da dama da suka hada da tashin hankali a Gabashi da kudancin ta, yayin da fari da amaliya kuma suka addabe ta.

Chadi ta taka rawa sosai wajen kai daukin soji a Mali da Janhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma yaki da kungiyar boko haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.