Isa ga babban shafi
Najeriya

Dalung ya ce wajibi ne takwarsa ta harkokin mata ta yi marabus

Bayan bayyana matsayinta na cewa tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar za ta mara wa baya a zaben shekarar 2019, ministar kula da harkokin mata Aisha Jummai Alhassan ta ce har yanzu tana biyayya ga shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Barr Solomon Dalung, ministan matasa da wasannin Najeriya.
Barr Solomon Dalung, ministan matasa da wasannin Najeriya. RFI/bashir
Talla

Sai dai ministan matasa da wasanni Solomon Dalung ya ce ba’a gudu da susar katara, saboda haka abin da ya fi dacewa shi ne Ministar ta aje aikin ta.

 

Ministan Dalung wanda ke zantawa da manema labarai, ya ce kalaman na minista Aisha na kara tabbatar da cewa akwai wadanda ke yi wa shugaban kafar angulu a kokarinsa na yi wa ‘yan Najeriya aiki.

 

Ministan matasan ya bayyana cewa Alhassan na nakasar da gwamnati ne, saboda haka kamata ya yi ta gaggauta barin wannan matsayi domin karbar matsayin daraktan yakin neman zaben wanda take son marawa a zaben na 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.