Isa ga babban shafi
KENYA

Bangaren shari'ar Kenya na da matsala- Kenyatta

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya caccaki bangaren shari’a na kasar wanda ya bayyana a matsayin matsalar da kasar ke fama da ita.

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta
Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta Service de presse de la présidence kényane
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Kotun Kolin kasar ta soke zaben da aka gudanar a watan jiya, in da aka bayyana Kenyatta a matsayin wanda ya yi nasara kan abokin hamayyarsa, Raila Odinga.

A cewar Kotun ta dauki matakin ne saboda makudin da aka tafka a zaben, kuma ta bada umarnin sake gudanar da wani sabon zaben cikin kwanaki 60, wato kafin ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa.

Duk da dai Kenyatta ya nuna adawa da hukuncin kotun amma ya ce, sai bi umarninta.

Sai dai ya lashi takobin yin garanbawul a bangaren shari’ar kasar da zaran an sake zaben sa.

Kenyatta ya kuma yi watsi da kiraye-kirayen ‘yan adawa da ke bukatar sauya jami'an hukumar zaben kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.