Isa ga babban shafi
Kenya

Kotun kolin Kenya ta soke zaben shugabancin kasar

Kotun Kolin Kenya ta soke zaben shugabancin kasar da aka gudanar a watan jiya, in da aka ayyana Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya yi nasara.

Magoya bayan jagoran 'yan adawa na kasar Kenya Raila Odinga, yayinda suke murna kan matakin kotun kolin kasar, na soke zaben shugabancin kasar da ya bai wa shugaba mai ci Uhuru Kenyatta nasara kan Odinga, ranar 1 ga Satumba 2017.
Magoya bayan jagoran 'yan adawa na kasar Kenya Raila Odinga, yayinda suke murna kan matakin kotun kolin kasar, na soke zaben shugabancin kasar da ya bai wa shugaba mai ci Uhuru Kenyatta nasara kan Odinga, ranar 1 ga Satumba 2017. REUTERS/James Keyi
Talla

A cewar Kotun ta dauki matakin ne sakamakon kura-kuren da aka samu a zaben, yayin da ta bada umarknin sake gudanar da wani zaben cikin kwanaki 60.

Sai dai shugaba Uhuru Kenyatta ya ki amince wa da hukucin kotun, amma duk da haka zai mutunta umarninta kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

Shi kuwa babba abokin hamayyar Kenyatta, wato Raila Odinga ya yaba da matakin Kotun, wanda y ace, shi ne irinsa na farko a nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.