Isa ga babban shafi
Najeriya

EFCC ta karbo Naira biliyan 409 a shekara daya

Shugaban Hukumar EFCC a Najeriya Ibrahim Magu ya ce sun yi nasarar karbo sama da naira biliyan 409 da Dala miliyan 69 a cikin shekara guda duk da matsalolin da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu.

Shugaban EFCC Ibrahim Magu.
Shugaban EFCC Ibrahim Magu. premiumtimesng.com
Talla

EFCC ta kuma kwato kudi sama da dala miliyan 69 daga sassan kasar da aka sace da kuma wasu makudan kudaden kasashen waje da suka hada Fam da yuro da kuma Riyal da Dirham

EFCC ta kwato kudaden ne daga watan Janairu zuwa Agustan bana.

Magu ya ce kudaden sun hada da nasarar da suka samu a kotu wajen karbe kudin tsohuwar ministan mai Dieziani Allison Maduekwe bayan dukiyar wasu jihohi da suke aiki akai.

Kananan hukumomin Najeriya na daya daga cikin yankunan da ake zargi da yin almubazzaranci da dukiyar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.