Isa ga babban shafi
Afrika

Bankin raya Afrika zai zuba jarin bunkasa aikin noma a Afrika

Bankin raya kasashen Afirka ya ce zai zuba jarin Dala biliyan 24 nan da shekaru 10 domin ganin nahiyar Afirka ta bunkasa aikin noma da samar da abinci maimakon dogaro da kasashen duniya.

Shugaban Bankin Raya Afrika Akinwunmi Adeshina tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Bankin Raya Afrika Akinwunmi Adeshina tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari thenewsnigeria
Talla

Shugaban Bankin Akiwunmi Adeshina wanda ya bayyana haka ya ce za a kaddamar da shirin ne a karkashin shirin bankin mai taken Ciyar da Afirka.

Adeshina ya kuma ce bankin yana kokarin ganin ya samarwa manoma kasuwannin da suka dace da za su dinga taimaka wa manoman wajen samun ribar amfanin gona sabanin yadda ‘yan kasuwa ke yi.

A ranar 4 ga Satumba Bankin raya Afrika zai jagoranci wani babban taron nazarin raya Afrika a Abidjan a bangaren wadatuwar abinci da samar da ayyukan yi a fannin noma.

Bankin yana fatar kashe dala tiriliyan 1 zuwa 2030 a karkashin shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.