Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Jamhuriyar Congo: Sama da mutane miliyan 3 sun rasa muhallansu

Majalisar Dinkin Duniya ta koka bisa yadda ta ce yawan fararen hula, da rikicin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya raba da muhallansu ya ninka cikin watanni 6.

Wasu daga cikin mutanen da suka rasa muhallansu a Jamhuriyar Dimokardiyyar Congo, sakamakon barkewar sabon fada a yankin Kasai.
Wasu daga cikin mutanen da suka rasa muhallansu a Jamhuriyar Dimokardiyyar Congo, sakamakon barkewar sabon fada a yankin Kasai. citizen.co.za
Talla

Jami’in da ke Magana da yawun hukumar lura da ‘yan gudun hijira ta majalisar George OKoth-Obbo y ace yawan wadanda suka tsere daga gidajensu a yanzu yah aura miliyan 3 da 800,000.

Zalika Obbo ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, akalla mutane miliyan daya da dubu 400 ke bukatar abinci da kayayyaki a yankin Kasai inda sama da mutane 3,000 suka hallaka sakamakon sabon fadan da ya barke tsakanin sojin Jamhuriyyar Kongo da ‘yan tawaye.

Zalika wani rahoton yace ana fuskantar wani tashin hankalin tsakanin kungiyoyin yan tawaye da ke adawa da juna, a lardin Tanganyika da ke kudu maso gabashin kasar, lamarin da ya tilastawa dubban fararen hula tserewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.