Isa ga babban shafi
Angola

Ana zaben shugaban kasa a Angola

An bude runfunan zaben shugaban kasa a Angola, zaben da zai kawo karshen mulkin Jose Eduardo Dos Santos wanda ya shafe shekaru kusan 40 yana shugabanci a kasar.

Al'ummar Angola na zaben shugaban kasa wanda zai kawo karshen mulkin shugaba Dos Santos
Al'ummar Angola na zaben shugaban kasa wanda zai kawo karshen mulkin shugaba Dos Santos REUTERS/Siphiwe Sibeko/File Photo
Talla

Rahotanni sun ce an samu tsaikun bude runfunan zaben a Luanda babban birnin kasar.

Duk da dai Dos Santos ya kauracewa tsayawa takara amma ana sa ran dan takarar Jam’iyyarsa ta MPLA zai lashe zaben.

Ana ganin zaben dai a matsayin wani makamin tabbatar da sauyi a Angola, bayan shugaba Dos Santos ya ki yin tazarce wanda ya shafe shekaru kusan 40 yana mulki a kasar.

Sai dai Mutanen Angola da kuma masu lura da siyasar kasar na ganin babu makawa Joao Lourenco Dan takarar jam’iyya mai mulki ta shugaba Dos Santos ne zai lashe zaben.

Kodayake wasu na ganin matasa da ke son canji na iya ba jam’iyya mai mulki mamaki musamman ganin yadda matasan suka fito suna goyon bayan manyan jam’iyyun adawar kasar guda biyu.

Tuni dai ‘yan adawa da wasu ‘yan rajin kare hakkin bil’adama suka bayyana shakku akan makomar sakamakon zaben saboda yadda aka mika takardun zaben ga sarakunan gargajiya.

Tun samun ‘yancin Angola a 1975 daga Portugal Dos Santos ke shugabanci a Angola

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.