Isa ga babban shafi
Africa

Sama da 'yan kasar Habasha miliyan 7 na bukatar agaji

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa miliyoyin ‘yan kasar Habasha suna bukatar agajin gaggawa, biyo bayan matsanancin farin da suka fuskanta da kuma ambaliyar ruwan da ta lalata amfanin gona da sanadin mutuwar dabbobi masu yawan gaske.

Wani dan kasar Habasha da ke tafiya a daf da inda wata saniya ta mutu sakamakon yunwa a yankin Farado Kebele dake kan iyakar kasar Habasha da Somalia.
Wani dan kasar Habasha da ke tafiya a daf da inda wata saniya ta mutu sakamakon yunwa a yankin Farado Kebele dake kan iyakar kasar Habasha da Somalia. Tiksa Negeri/Reuters
Talla

Rahoton da majalisar ta fitar ya ce akalla ‘yan kasar ta Habasha miliyan 7 da dubu dari 8 ne ke karbar agajin gaggawa na abinci, tun daga watan Afrilu zuwa yanzu, bayan yawan mutanen da ke bukatar taimakon ya karu daga miliyan 5 da dubu dari 6 a farkon wannan shekara.

A watan Yulin da ya gabata, alkalumma sun nuna cewa akwai kananan yara, ‘yan kasa da shekaru 5, dubu 376,000, da ke fama da yunwa a kasar, yayinda wasu miliyan 3 da dubu 600 da matan masu shayarwa ke cikin hadarin fadawa cikin tsananin yunwar.

A gefe guda kungiyar bada agaji ta Oxfam, ta yi gargadin cewa dole ne kasashen duniya da suka karkata kan batutuwan ISIS, Donald Trump da Korea ta Arewa su maido da hankulansu kan Habasha domin kaucewa aukawar kasar cikin mummunan yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.