Isa ga babban shafi
Kenya

Kenya: Raila Odinga ya garzaya kotun koli

Jagoran ‘yan adawar kasar Kenya Raila Odinga, ya shigar da kara kotun kolin kasar, don kalubalantar sakamakon zaben shugabancin kasar da ya bai wa shugaba mai ci Uhuru Kenyatta nasara.

'Yan adawa a Kenya sun kalubalanci sakamakon zaben shugabancin kasar a Kotu.
'Yan adawa a Kenya sun kalubalanci sakamakon zaben shugabancin kasar a Kotu. Reuters
Talla

Hukumar zaben kasar Kenya dai ta bayyana cewa Uhuru Kenyatta ya samu nasarar lashe zaben da ya gudana a ranar takwas ga watan Agustan da muke ciki, da kuri’u miliyan daya da dubu dari hudu, sakamakon da Odinga yayi watsi da shi, bisa ikirarin an tafka magudi cikinsa.

A halin yanzu dai matakin Raila Odinga na komawa ga kotu, maimakon jagorantar zanga-zanga, ya sanya hakulan ‘yan kasar ta Kenya sun kwanta, idan akai la’akari da yadda akalla mutane 1,200 suka rasa rayukansu biyo bayan rikicin da ya barke bayan zaben shugabancin kasar da aka yi a shekarar 2007.

Ko a waccan lokacin dai sai da Odinga ya koma kotu, sannan aka samu rikicin ya lafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.