Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu- Uganda

Yan gudun hijirar miliyan daya ne suka tsere daga Sudan ta Kudu

Majalisar dinkin duniya ta ce yawan ‘yan gudun hijirar da suka tsere daga Sudan ta Kudu zuwa kasar Uganda, ya zarta miliyan daya.

Wasu tsofinJami'an sojin kasar Sudan ta Kudu
Wasu tsofinJami'an sojin kasar Sudan ta Kudu REUTERS/Jok Solomun
Talla

Alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar na kunshe ne cikin sabon rahoton da ta fitar a baya-bayanan, wanda kuma cikinsa ta yi gargadin cewa akwai bukatar samar da kudade, domin agazawa wadanda rikicin kasar Sudan ta kudun ya dai-daita cikin hanzari.

Majalisar dinkin duniyar ta ce, akalla wasu ‘yan gudun hijirar sama da miliyan dayan ne suka tsere zuwa kasashen Kenya, Habasha, Jamhuriyar Congo da kuma jamhuriyar afrika ta tsakiya daga sudan ta kudun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.