Isa ga babban shafi
Burundi

Harin gurneti ya raunata mutane a Burundi

Rundunar ‘yan Sandan kasar Burundi ta ce akalla mutane 29 sun jikkata, yayinda mutun daya ya rasa ransa a wani harin gurneti da aka kai cikin babban birnin kasar Bujumbura, a daren jiya Alhamis.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ????
Talla

Kakkakin ‘yan sandan kasar Pierre Nkrukiye, ya ce an kai harin ne kan wata mashaya da ke yankin Buyenzi a babban birnin, ya zuwa yanzu ba’a gano wanda yake da hannu wajen kai shi ba,

Tun a watan Afrilun shekara ta 2015, Burundi ta fada cikin rikicin siyasa, bayanda shugaban kasar Pierre Nkrunziza, ya sanar da aniyarsa ta sake neman shugabancin kasar, wa’adi na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.