Isa ga babban shafi
Mali

Kaddamar da rundunar sojin Sahel sai da taimakon kasashen Duniya

Kasar Mali ta bukaci taimakon kasashen duniya wajen samun kudade da makamai domin kaddamar da rundunar sojin Sahel wadda za ta yi yaki da yan ta’adda dake ci gaba da kai munanan hare hare a Yankin.

Ibrahim Boubacar Keita shugaban kasar Mali  a lokacin ganawarasa da Minstan tsaron Faransa
Ibrahim Boubacar Keita shugaban kasar Mali a lokacin ganawarasa da Minstan tsaron Faransa HABIBOU KOUYATE / AFP
Talla

Jakadan Mali a Majalisar Dinkin Duniya Issa Konfourou, ya shaidawa kwamitin Sulhu cewar harin da aka kai Burkina Faso da ya hallaka mutane 18 da wanda aka kai Mali da ya kashe mutane 9 ya dada tababtar da muhimancin kaddamar da rundunar sojoji 5,000 da kasashen Nijar da Mali da Chadi da Mauritania da kuma Burkina Faso zasu bada gudumawar soji.

Ita dai wannan runduna na bukatar kudin da ya kai dala kusan miliyan 500 kafin fara aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.