Isa ga babban shafi
Congo

Congo Brazaville na fuskantar matsalar tattalin arziki

Shugaban Kasar Congo Dennis Sassou Nguesso yace kasar sa na fuskantar matsalar tattalin arziki sakamakon faduwar farashin mai a kasuwanni duniya.

Sassou Nguesso Shugaban kasar Congo Brazaville
Sassou Nguesso Shugaban kasar Congo Brazaville STRINGER / AFP
Talla

Yayin da yake jawabin bikin cika shekaru 57 da samun yancin kai, shugaban kasar yace kasar na fuskantar matsaloli da dama, kuma babu dalilin boye su ga jama’a.

Nguesso da ya jagoranci kasar Congo na shekaru 30 yace babu yadda za’a magance irin wadanan matsaloli ba tare da zaman lafiya ba, inda ya bukaci shugaban yan tawayen kasar Frederic Bitsamou da ya mika kan sa ga jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.