Isa ga babban shafi
Saliyo

Saliyo na neman agajin gaggawa bayan ambaliyar ruwa

Shugaban Saliyo Ernest Bai Koroma ya bukaci taimakon gaggawa ga babban birnin Freetown na kasar, in da mutane sama da 300 suka rasa rayukansu sakamaon ambaliyar ruwa da zabtarewar laka.

Ambaliyar ruwan Saliyo da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 300 a Freetown
Ambaliyar ruwan Saliyo da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 300 a Freetown REUTERS/ Ernest Henry
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da tono gawarwakin mutanen da laka ta binne a gidajensu.

Baya ga wadanda suka mutu, akwai kuma mutane dubu 3 da suka asa muhallansu a ibtila’in, yayin da ake shirin haka manyan kaburbura don binne tarin gawarwaki wuri guda.

Rahotanni na cewa, dakunan ajiye gawarwakin sun cika makil a birnin na Freetown.

A halin yanzu dai ana ci gaba da kokarin gano wadanda ke da sauran numfashi da lakar ta binne.

Amma dai ana fargabar karuwar alkaluman mutanen da suka mutu a ibtila’in kamar yadda ma’aikatan jin-kai suka bayyana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.