Isa ga babban shafi
Burkina-Faso

An kashe mutum 18 a harin ta'addanci a Ouagadougou

Gwamnatin Burkina Faso ta ce an kawo karshan Kazamin harin da wasu ‘yan bindiga suka kaddamar a gidan sayar da abinci tare da hallaka mutane 18 a birnin Ouagadougou.

Jami'an tsaro sun kashe Mahara biyu da suka kai hari gidan abinci a Ouagadougou
Jami'an tsaro sun kashe Mahara biyu da suka kai hari gidan abinci a Ouagadougou REUTERS/Reuters TV
Talla

Ministan sadarwa kasar, Remis Dandjinou, ya sanar da samun nasaran harbe biyu daga cikin ‘yan ta’addan da suka kaddamar da harin tun a daren jiya lahadi, tare da jikkata wasu mutane 8.

Mista Remis da ke shaidawa al’ummar kasar halin da ake ciki ta kafar talabijin, ya ce an kai harin ne gidan sayar da abincin mutanen Turkiya, kuma jami’an tsaro na ci gaba da bincike.

Wani soja ya shaidawa wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa cewar akwai mutanen da akayi garkuwa da su a hawa na daya da na biyu na ginin.

Magajin Garin Ouagadougou da ministocin gwamnati sun ziyarci inda aka kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.