Uhuru Kenyatta ya lashe zaben kasar
Sakamakon zabe na karshe daga Shugaban Hukumar zaben Kenya na tabbatar da Shugaban kasar Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben .
Wallafawa ranar:
Uhuru Kenyatta ya samu kashi 54,24 cikin dari na kuri’u da aka kada , Jagoran adawa Raila Odinga wanda ke ikirarin samun nasara ya samu kashi 44 da dugo 74.
Masu sa idanu kan zaben na cewa an yi zaben cikin kwanciyar hankali bayan ga tarzoma da aka samu bayan fara sanar da sakamakon zaben.
Uhuru Kenyatta yan lokuta da sanar da sakamakon zaben ya yi kira zuwa yan kasar dama yan adawa na gani sun kai zuciya nisa tareda yi na’am ga goron gayyata domin ci gaba da yiwa kasar aiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu