Isa ga babban shafi
Bakin-haure

Bakin-haure 300 aka jefa a tekun Yemen

Kungiyar da ke sa ido kan kauran baki ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce baki 56 'yan asalin Afirka ne suka nitse a tekun Yemen cikin sa’oi 24, yayin da wasu da dama suka bata bayan masu safarar su sun tilastawa wasu 300 fadawa ruwa daga cikin jirage biyu.

Bakin-hauren da suka isa gabar ruwan Yemen
Bakin-hauren da suka isa gabar ruwan Yemen SALEH AL-OBEIDI / AFP
Talla

Kungiyar ta ce ‘yan kasashen Habasha da Somalia da suka yi sa’ar isa gabar ruwan Shabwa da ke Yemen sun yi Karin haske kan yadda wadanda suka dauke su a kwale-kwalen suka dinga tilasta musu afkawa cikin teku saboda kaucewa jami’an tsaro.

Mai Magana da yawun kungiyar ya ce a jiya kawai mutane 6 suka mutu bayan an tilastawa baki ‘yan kasar Habasha 180 barin jirgin ruwan, yayin da 13 kuma suka bata.

Kafin wannan a ranar laraba, baki akalla 50 suka mutu, wasu 22 suka bata lokacin da irin wadanan mutane suka tilastawa baki ‘yan kasar Somalia fadawa tekun.

Jami’an kungiyar da na kungiyar agaji ta Red Cross sun yi nasarar gano gawawaki 29 da aka birne a wani rami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.