Isa ga babban shafi
Kamaru

‘Yar India ta ceto matan Kamaru da ake tilastawa karuwanci

Wata Mace ‘yar assalin kasar India da ke aikin bishara ta yi nasarar ceto ‘yan matan kasar Kamaru sama da 200 da aka tilastawa aikin karuwanci a Gabas ta Tsakiya bayan an dirka musu kwaya.

Vanaja Jasphine mai shekaru 39 ta kasance 'yar India da ke fafutikar kare hakkin dan adam
Vanaja Jasphine mai shekaru 39 ta kasance 'yar India da ke fafutikar kare hakkin dan adam REUTERS
Talla

Vanaja Jasphine ta ce ta gano wadanan ‘yan matan ne da aka yi safarar su daga kamaru zuwa Gabas ta Tsakiya da sunan sama musu aikin yi.

Jasphine na daya daga cikin wadanda aka karrama a Amurka saboda rawar da ta ke takawa wajen yaki da safarar mutane.

Kwashe mata daga kasashen Afirka zuwa ketare domin karuwanci na sake tsananta duk da matakan da ake dauka wajen dakile irin wannan safarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.