Isa ga babban shafi
Democratic Republic of Congo

An halaka masu adawa da Joseph Kabila 27

KUNGIYAR Kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch tace mutane 27 cikin su harda Yan Sanda 3 aka kashe a arangamar da akayi lokacin zanga zangar adawa da gwamnatin shugaba Joseph Kabila a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo.

Dubban mutane ne ke adawa da Gwamnatin shugaba Joseph Kabila a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo tun baya da ya hau kujerar naki a lokacin da wa'adin mulkinsa ya kare a cikin watan Disamban bara
Dubban mutane ne ke adawa da Gwamnatin shugaba Joseph Kabila a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo tun baya da ya hau kujerar naki a lokacin da wa'adin mulkinsa ya kare a cikin watan Disamban bara Reuters
Talla

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce an kashe akasarin yayan kungiyar Bundu dia Kongo da suka shiga zanga zangar ne a birnin Kinshasa lokacin da su kayi taho mu gama da Yan Sanda a cikin wannan mako.

Kungiyar ta BDK guda ce daga cikin jerin kungiyoyin da ke neman ganin bayan shugaba Joseph Kabila wanda ya kekashe kasa yaki sauka daga karagar mulki duk da cewa ya kammala wa’adin mulkin sa zagaye na biyu.

Mai Magana da yawun Yan Sanda ya tababtar da kashe mutane 19 akasarin su yayan kungiyar ta BDK.

Daraktan kungiyar kare hakkin Bil Adaman dake kula da Yankin Afirka ta Tsakiya, Ida Sawyer, yace ana bukatar sahihin binciken gaggawa domin gano wadanda suka aikata kisan da niyyar hukunta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.