Isa ga babban shafi
Oxfam

''Akasarin Bakin-haure na fuskantar fyade da azabtarwa''

Kungiyar bada agaji ta Oxfam ta bayyana cewa, akasarin ‘yan Afrika da ke ratsawa ta Libya don zuwa kasashen Turai, sun fuskanci cin zarafi, azabtarwa da kuma fyade.

Kafin ‘yan ci-rani su ratsa ta tekun ana kwace musu guzuri  da yi musu fyade- Oxfam
Kafin ‘yan ci-rani su ratsa ta tekun ana kwace musu guzuri da yi musu fyade- Oxfam REUTERS/Jesus Moron
Talla

Oxfam ta kuma bukaci kasashen Turai da su samar da nagartattun hanyoyi ga masu kokarin tsallakawa zuwa Turai don samun ingantacciyar rayuwa.

Kasar Libya ta kasance wata babbar hanyar da ‘yan ci-rani ke ratsawa ta tekun Mediterranean zuwa kasashen Turai , in da a cikin wannan shekara ‘yan Afrika dubu 95 suka ratsa ta hanyar, yayin da a bara, aka samu mutane 180.

Kafin dai ‘yan ci-ranin na Afrika su ratsa ta tekun, ana kwace musu guzuri , da yi musu fyade gami da tsare su a gidan yari a kasar.

Kazalika ana tirsasa wa wasunsu shiga aikin karfi tare da kungiyoyin ‘yan daba masu dauke da makamai.

‘Yan ciranin da suka isa Italiya, sun shaida wa kungiyar Oxfam cewa, an garkame su a wani gidan yari cike da gawarwakin mutane a Libyar.

Har ila yau, ‘yan ci-ranin sun ce, an tirsasa musu kiran danginsu ta wayar tarho don neman kudin fansa kafin sakin su.

Akwai kuma wadanda aka yi musu dukan tsiya tare da hana su abinci na tsawon watanni.

Shugaban Oxfam a Italiya, Roberto Barbieri, ya ce, wadannan mutane da aka musgunawa a Libya na kokarin gujewa yake-yake ne da cin zarafi a kasashensu , amma suka sake fada wa cikin wani tashin hankali a Libya.

ya ce, dole ne kungiyar Tarayyar Turai ta samar da nagartattun hanyoyi ga ‘yan afrikan da ke ratsawa ta Libya zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.