Isa ga babban shafi
Togo

Zanga-zangar yan Adawa a Lome na kasar Togo

Dimbin magoya bayan ‘yan adawa ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Lome na kasar Togo, inda suke neman shugaban kasar Faure Gnasimgbe ya amince domin a aiwatar da sauye sauye na siyasa a kasar, wadanda za su bayar da damar takaita wa’adin shugabancin kasar.

Faure Gnassingbé Shugaban kasar Togo
Faure Gnassingbé Shugaban kasar Togo AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

Yanzu haka dai a karkashin kundin tsarin mulkin kasar, shugaban kasar na da damar sake tsayawa takara a duk lokacin da yake bukata ba tare da kayyade wa’adin ba.

Shugaban yan adawa Jean Pierre Fabre da jimawa ya bukaci manyan kasashen Duniya su tsoma hannu a batun siyasar kasar ta Togo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.