Isa ga babban shafi
Rwanda

Shugaba Paul Kagame na iya zarcewa a zango na uku

Alamu na nuni da cewa shugaban Rwanda mai ci Paul Kagame na iya yin nasara kan sauran ‘yan-takarar shugabancin kasar biyu da ke fafatawa a babban zaben kasar na yau.An dai bai wa al’ummar kasar kimanin mutum milyan 7 damar kada kuri’unsu har tsawon awanni takwas tun daga misalin karfe 8 na safiyar yau.

Shugaban Rwanda Paul Kagame
Shugaban Rwanda Paul Kagame REUTERS/Jean Bizimana
Talla

Tun da misalin karfe uku na yammacin yau ne aka dakatar da shiga layin kada kuri’ar yayinda aka bada dama ga wadanda suka kasance kan layi kafin lokacin damar ci gaba da kada kuri’unsu.

A cewar shugaban hukumar zaben kasar Charles Munyaneza al’umma sun fitowa zaben yadda ya kamata, haka kuma ba a samu tashe-tashen hankula a sassan kasar dalilin zaben ba.

Rahotanni sun ce al’ummar kasar sun yi ado da launin shudi, da ruwan dorawa da kuma kore wanda ke nuna kalolin tutar kasar tare kuma da jeruwa cikin da a a runfunan da aka ware don kada kuri’ar.

Shugaba Kagame mai shekaru 59 ya kada kuri’ar sa da tsakiyar ranar yau tare da rakiyar mai dakinsa da kuma yaransa hudu bisa cikakken tsaro a rumfar daya kada kuri’ar, a dai-dai lokacin da masu shela ke kira ga al’ummar kasar don fitowa su kada kuri’a.

Wannan dai shi ne karon farko da jam’iyyar adawa ta fito aka fafata da ita a zaben kasar tsawon shekaru 23 tun baya da Kagame ya karbe iko kuma majalisar kasar ta amince da shi a shekarar 2000.

Kafin yanzu dai jam’iyyun kawance ko kuma masu mara baya ga Kagame ne kadai ke samun damar fafatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.