Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Kungiyar Fulani ta ruga kotun ECOWAS kan kisan Mambilla

Kungiyar Fulani makiyaya ta Gan Allah ta ruga kotun kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS domin neman hakkinsu kan kisan da aka wa mambobinta a Mambilla a Jihar Taraba arewacin Najeriya.

Fulani makiyaya a Najeriya
Fulani makiyaya a Najeriya RFI Hausa/Awwal
Talla

Wannan na zuwa ne bayan dakatar da shugaban karamar hukumar Sardauna da ke Jihar Taraba a ci gaba da binciken da kwamitin da Gwamnatin Jihar ta kafa ya gudanar.

Sakatare Janar na kungiyar Fulanin ta Gan Allah, Alhaji Saleh Bayari ya shaidawa RFI Hausa cewa sun ruga kotun ECOWAS ne don neman hakkin mambobinsu da aka kashe.

A ranar 17 ga wannan watan na Yuli ne aka kashe Fulanin makiyaya kusan 50 da suka hada da mata da yara kanana a Mambilla cikin karamar hukumar Sardauna a Jihar Taraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.