Isa ga babban shafi
Senegal

Ana shirin gudanar da zaben 'yan majalisa a Senegal

A wannan juma’a ake kammala yakin neman zaben ‘Yan Majaisun kasar Senegal, yayin da ake shirin fafatawa tsakanin Jam’iyyar shugaba Macky Sall da ke neman rinjaye a Majalisar da tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade da kuma Magajin Garin Dakar Khalifa Sall.

Macky Sall, shugaban kasar Senegal
Macky Sall, shugaban kasar Senegal AFP PHOTO/SEYLLOU
Talla

Sakamakon arangamar da aka yi tsakanin magoya bayan shugaba Sall da na Magajin Garin Dakar, ‘yan Sanda sun kama mutane da dama.

Khalifa Sall yanzu haka na tsare a gidan yari saboda zargin almubazzaranci da kudin da yawansu ya kai dala miliyan 3, yayin da dan tsohon shugaban kasar Karim Wade ya samu mafaka a Qatar bayan an daure shi a kan mallakar dunkiyar da ta kai dala miliyan 198 ta hanyar da ba ta dace ba, bayan an yi masa sakin talala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.