Isa ga babban shafi
Nijar

An tsige magajin garin birnin Yamai daga mukaminsa

Taron majalisar ministocin da aka gudanar jiya alhamis a Jamhuriyar Nijar, ya dauki matakin tube magajin garin birnin Yamai Hassane Seydou daga mukaminsa.

Shugaban Nijar Issifou Mahamadou
Shugaban Nijar Issifou Mahamadou AFP/AFP
Talla

Duk da cewa ba a bayar da wani dalili a game da tube magajin garin ba, to amma a cikin makon da ya gabata shugaban kasar Issifou Mahamadou ya fito fili karara inda ya bayyana takaicinsa dangane da yadda shara ke neman mamaye birnin tare da cushewa magudanun ruwa, lamarin da ke haifar da ambaliyar ruwa a kowace damina a birnin.

A cikin watan yunin da ya gabata, taron majalisar ministocin kasar ya sanar da tsiga wasu zababbin magadan gari shida wadanda aka zarga da handame dukiyar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.