Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Tsutsa na cinye amfani gona a Sudan ta Kudu

Majalisar dinkin duniya ta ce bullar wata tsutsa mai lalata amfanin gona, wadda ta fara cinye gonaki a sassan nahiyar Afrika, zata kara tsananta matsalar yunwa da kasar Sudan ta Kudu ke fama da ita.

Tsutsar da ke cinye amfani gona a Sudan ta Kudu
Tsutsar da ke cinye amfani gona a Sudan ta Kudu
Talla

Hukumar samar da abinci ta FAO, da ke karkashin majalisar, ta tabbatar da bullar tsutsar a kudancin Equatorial, wanda yanki ne mafi muhimmanci ga Sudan ta Kudu a fannin noma, bayaga sauran sassan kasar.

Bayan Kudancin Equatorial da ke kan iyaka da kasar Uganda, sauran yankunan Sudan ta Kudun da wannan tsutsa ta fara lalata amfanin gona sun hada da, arewacin jihar Bahr el Gazal da kuma jihar Jonglei.

Tsutsar wadda ta fi barnata Masara, wake da sauran ire-irensu, tana iya tashi ta kuma yi tafiya mai nisan gaske, lamarin da yasa majalisar dinkin duniya bayyana fargabar cewa, tsutsar zata iya isa nahiyar Asiya da ma sauran yankunan da ke daf da Mediterranean nan da shekaru kalilan.

Wakilin hukumar ta FAO a Sudan ta Kudu, Serge Tissot ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Ruters cewa, bullar tsutsar zai haddasa karuwar tsadar kayan abinci, a kasar ke fama da shi, wanda kuma a halin yanzu akalla rabin al’ummar kasar basa samun isasshen abinci, kasancewar a shekarar da ta gabata ka dai sai da farashin kayan masarufi a kasar ya zarta kashi 800.

Rikicin kasar Sudan ta kudu da ya raba akalla mutane miliyan Uku da gidajensu ya takawa rawa wajen hana manoman kasar fita domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.