Isa ga babban shafi
Morocco

Kotun Morocco ta daure 'yan gwagwarmayar 'yancin Sahrawi

Kotu a Morocco ta yankewa wasu mutane 23 masu gwagwarmayar neman 'yancin kasar yammacin saharawi hukuncin zaman gidan yari da zai fara daga shekaru biyu zuwa rai da rai sakamakon kisan wasu jami’an tsaron kasar 11 a yammacin sahara.

Tun a shekarar 2013 ne wata kotun soji a Morocco ta yankewa masu faftukar hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20 zuwa rai da rai
Tun a shekarar 2013 ne wata kotun soji a Morocco ta yankewa masu faftukar hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20 zuwa rai da rai Farouk Batiche / AFP
Talla

Hukuncin ya biyo bayan fafutukar da masu kare hakkin dan-adam na duniya suka yi wajen ganin an tabbatar da adalci a shari’ar.

Morocco da 'yan gwagwarmayar neman yancin yammacin Saharar dai sun jima suna zargin juna da haddasa rikicin da ya kawo kisan mutane da dama tsakanin masu gwagwarmayar da kuma jami’an 'yan-sanda a sansanin ‘yan-gudun hijira dake Gdeim Izik cikin watan Nuwamban shekarar 2010.

Tun a shekarar 2013 ne wata kotun soji a Morocco ta yankewa masu faftukar hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20 zuwa rai da rai, lamarin da kungiyoyin kare hakkin dan adam na duniya suka bayyana da rashin adalci tare da bukatar mai da lamarin hannun kotun farar hula.

An dai tabbatar da hukuncin bayan shafe tsawon awanni 12 ana tattaunawa inda aka yankewa mutum 19 cikin 23 wa'adin shekaru 20 zuwa daurin rai da rai a gidan yari, hudu daga ciki kuma aka sassauta musu hukunci kasancewa tuni sun riga sun kammala wa adinsu kafin hukuncin tare kuma da basu damar daukaka kara kan hukuncin cikin kwanaki goma masu zuwa

Lamarin dai ya faru ne a ranar 8 ga Nuwamban 2010 lokacin da jami’an tsaron Morocco suka yi kokarin wargaza sansanin ‘yan-gudun hijira na Gdim Izik inda kuma a nan ne ‘yan gwagwarmayar neman yancin yammacin saharar ke zaune.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.