Isa ga babban shafi
Congo

Iyalan shugaban Congo na fuskantar tuhuma a Faransa

Hukumomin Shari’a a Faransa sun tuhumi dan ‘yar shugaban kasar Congo Brazzaville Dennis Sassou Nguesso da sarakuwarsa da laifin kashe kudaden jama’a Edgar Nguesso da mahaifiyarsa Catherine Ignanga sun gurfana a gaban kotu inda aka karanta musu laifufukan da ake tuhumar su akai.

Shugaban Congo Denis Sassou-Nguesso
Shugaban Congo Denis Sassou-Nguesso REUTERS/Anis Mili
Talla

Wannan ita ce tuhuma ta baya bayan nan da ake yi wa wasu daga cikin iyalan shugabanin kasashen Congo da Equatorial Guinea da Gabon a Faransa.

Tun shekarar 2010, masu bincike a Faransa ke ta kokarin tabbatar da kadarorin da iyalan suka mallaka a Faransa domin gurfanar da su a kotu.

A makon da ya gabata ne masu gabatar da kara a Faransa suka bukaci a kotu ta yanke wa mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodorin Obiang hukuncin daurin shekaru uku kan azurta kansa da kudaden talakawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.