Isa ga babban shafi
Libya

Libya ta kwato Benghazi daga hannu mayakan Jihadi

Rundunar sojin Libya ta sanar da kwato Benghazi daga ikon gungun mayakan Jihadi da suka kwace ikon birnin. Da suka hada da kungiyar IS da kuma Ansar al Shari’a mai alaka da al qaeda.

Libya ta sanar da kwato Benghazi daga ikon gungun mayakan Jihadi
Libya ta sanar da kwato Benghazi daga ikon gungun mayakan Jihadi REUTERS/Esam Omran Al-Fetori
Talla

An shafe tsawon shekaru uku ana yakin kwato Benghazi daga hannun mayakan bayan zanga-zangar da ta kawo karshen mulkin Kanal Ghaddafi.

Babban kwamandan sojin Libya ne Khalifa Haftar ya sanar da kwato birnin na Benghazi a kafar telebijin din kasar.

A cikin jawabinsa ya ce ‘’bayan shafe shekaru ana gwabza yaki a shekaru uku, a yau an yi nasarar kwato Benghazi’’.

Ya kara da cewa yanzu sabon babi ne aka bude na tabbatar da zaman lafiya da tsaro da sasantawa da kuma sake gina kasa tare da girmmama sojojin da suka sadaukar da ransu domin kwato garin na Benghazi.

An kaddamar da farmakin kwato garin ne dai akan gungun mayakan jihadi na Benghazi da suke samun goyon bayan mayakan IS a Libya da kungiyar Ansar al Shura mai alaka da al Qaeda.

Kwamadan na Libya da ya sanar da kwato garin Benghazi baya goyon bayan gwamnatin Tripoli da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita inda ya ke marawa gwamnatin gabashin Libya masu ra’ayin tsohon shugaba Kanal Ghaddafi.

Libya dai ta kasa samun zaman lafiya tun kawar da shugaba Ghaddafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.