Hukumomin Kasar Congo Sun Sanar Da Babu Cutar Ebola A Kasar
Kasar Jamhuriyar Democradiyya ta Congo yau Asabar ta sanar da cewa ta yi bankwana da sake bullar cutar Ebola tun daga yau, kasancewar kwanaki 42 ke nan cur ba’a ji labarin sake bullar cutar ba.
Wallafawa ranar:
A kasar Congo inda aka fara samun cutar cikin shekara ta 1976, aka sake samun bullar cutar kwanakin baya inda aka ce ta kashe mutane takwas.
Ministan Lafiya na kasar Oly Ilungu ya sanar cikin wata sanarwa cewa yanzu an tabbatar da cewa babu sauran cutar a fadin kasar.
Jimi'llan mutane dubu sha daya da dari uku suka mutu a lokacin da cutar ta barke sosai a yammacin Africa a shekara ta 2014.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu