Isa ga babban shafi
Nijar

Boko Haram ta kai hari sansanin ‘Yan gudun hijira a Diffa

Wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake sun tayar da bam a wani sansani da ke garin Kabalewa a jihar Diffa da ke gabashin Jamhuriyyar Nijar inda suka tarwatsa kansu tare da kashe wasu fararen hula biyu a sansanin.

Yankin Diffa na cikin dokar ta baci a Nijar domin yaki da Boko Haram
Yankin Diffa na cikin dokar ta baci a Nijar domin yaki da Boko Haram Nicolas Champeaux pour RFI
Talla

Kabalewa, gari ne da ke karbar dubban ‘yan gudun hijirar Boko Haram, kuma mafi yawansu sun fito daga Najeriya.

Wani mazauni garin na Kabalewa ya shaidawa RFI Hausa cewa wasu mata ne guda biyu suka shiga sansanin ‘yan gudun hijira suka tarwatsa kansu, kuma harin ya kashe mutane biyu da jikkata wasu da dama.

Ya ce Matan sun kai harin ne a Masallacin sansanin na ‘yan gudun hijira.

Jihar Diffa dai na cikin dokar ta-baci da gwamnatin Nijar ta kafa domin yaki da ‘yan Boko Haram da suka jima suna kai hare hare a yankin.

Dubban ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram daga Najeriya ne suka tsallaka zuwa Nijar yawancin daga jihohin Yobe da Borno da ke makwabtaka da Diffa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.