Bakonmu a Yau
Majalisar Dinkin Duniya zata janye dakarunta daga Cote d'Ivoire
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:20
A gobe juma’a ne rundunar samar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, zata nade komatsanta domin ta fice daga cikin kasar Cote d’Voire bayan share tsawon shekaru 13 na aikin wanzar da zaman lafiya a wannan kasa dake yankin yammacin Afrika. Don jin irin rawar da rundunar ta taka a wajen aikin samar da zaman lafiya a wannan kasa, Abdoulaye Issa ya nemi jin ta bakin Adamu Zakari masanin siyasar kasashen Afrika ta Yamma.