Isa ga babban shafi
Najeriya

Kamaru ta sake taso keyar ‘Yan Najeriya 887

Kamaru ta dawo da ‘Yan Najeriya da suka tsere wa rikicin Boko Haram ya su 887 zuwa garin Banki, wanda ke gaf da iyakar kasashen biyu a wani mataki da aka ce an dauke shi ne da amincewar gwamnatin Najeriya.

'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a Jihar Borno
'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a Jihar Borno REUTERS/Paul Carsten
Talla

A watannin baya ne aka kulla yarjejeniya kan yadda za a dawo da ‘yan gudun hijirar zuwa gida amma da amincewarsu, yarjejeniyar da aka kulla karkashin kulawar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Honarabul Muhammad Sani Zoro, shugaban kwamitin kula da matsalolin yankin arewa maso gabashin Najeriya mai fama da rikicin Boko Haram, ya ce akwai dalilai biyu dangane da dawowar ‘yan gudun hijirar zuwa gida.

A cewarsa Kamaru ta dade tana keta yarjejeniyar Yaounde da aka amince wajen tasa keyar ‘yan gudun hijirar zuwa Najeriya duk da cewa alhakin kula da su ya rataya akan wuyanta a matsayinsu na ‘yan gudun hijira.

Sannan ‘Yan gudun hijirar na amincewa ne su dawo saboda an samar da tsaro a garuruwansu daga barazanar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.