Isa ga babban shafi
Mali-Sweden

Al-Qaeda ta saki wani dan Sweden da ta sace a 2011 a Mali

Gwamnatin Sweden ta tabbatar da sakin wani dan asalin kasar da kungiyar Al-Qaeda ta yi garkuwa da shi tun shekarar 2011 a Mali. Sai dai har yanzu babu cikakken bayani game da makomar wani dan asalin Afrika ta Kudu da kungiyar ta yi garkuwa da su tare bayan ta sace su a Timbuktu.

Johan Gustafsson da Al-Qaeda ta sace a shekarar 2011 a Mali
Johan Gustafsson da Al-Qaeda ta sace a shekarar 2011 a Mali AL JAZEERA / AFP
Talla

Ministar Harkokin Wajen Sweden Margot Wallstrom ta shaida wa manema labarai cewa, Mr. Johan Gustafsson da Al-Qaeda ta yi garkuwa da shi a Mali tun shekarar 2011 ya koma gida, cikin iyalansa.

Ministar ta nuna wa ‘yan jarida hoton Gustafsson tare da iyalansa, in da ta ce, yana cikin koshin lafiya.

Sai dai Uwargida Wallstrom ba ta bada cikakken bayani ba kan hanyar da Sweden ta bi wajen ‘yanto Gustafsson.

Amma ta ce, jami’an ‘yan sanda da ‘yan siyasa da jakadu da kuma hukumomin wasu kasashe sun taka rawa wajen ‘yanto mutumin.

Kazalika, Ministar, ba ta ce komai ba kan ko an biya kudin fansa kafin sakin shi ko kuma a’a.

A cikin watan Nuwamban 2011 ne, aka sace Gustafsson mai shekaru 42 tare da wani dan asalin Afrika ta Kudu, Stephen McGown da kuma wani dan kasar Netherland, Sjaak Rijke a birnin Timbuktu da ke arewacin Mali.

Amma a cikin watan Aprilun 2015 ne, dakarun Faransa na musamman suka ceto Rijke daga hannun kungiyar, yayin da har yanzu ba a san makomar McGown ba, kamar yadda mahaifinsa ya shaida wa kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.