Isa ga babban shafi
Uganda

Uganda ta samu tallafin kula da ‘yan gudun hijirar Sudan ta kudu

Kungiyar Tarrayar Turai ta dau alkawalin bayar da tallafin kudi miliyan 85 na yuro ga Uganda domin dawainiya da ‘yan gudun hijirar kasar Sudan ta kudu miliyan guda, da ke ci gaba da kwarara a cikin kasar.

'Yan gudun hijirar Sudan ta kudu a wani sansaninsu da ke Uganda
'Yan gudun hijirar Sudan ta kudu a wani sansaninsu da ke Uganda REUTERS/Stringer/File photo
Talla

Wannan sanarwa dai na zuwa ne a yayin da ake gudanar da taron gidauniya ga ‘yan gudun hijirar a birnin Kampala na Uganda, domin samar da kudi kimanin yuro miliyan biyu a shekara mai zuwa.

Babban sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijirar a arewacin Uganda, kuma a yau Juma’a zai hadu da wasu manyan jam’ian gwamnati da masu bada tallafi, hadi da shuwagabanin addini a kokarin da ake yi na samun damar hada kudaden da ake bukata.

Wadanda suka shirya wannan taro gidauniyar na bukatar ganin sun hada kimanin miliyan 8 yuro ne a cikin shekaru hudu masu zuwa

Kasar Uganda ta fada cikin matsananciyar matsalar ‘yan gudun hijira sakamakon yadda suke kwarara daga Sudan ta kudu da ke tserewa yakin basasar tsawon shekaru uku da rabi da ya mamaye jaririyar kasar da ke yankin gabashin nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.